A jiya Alhamis ne ake gudanar da bikin kaddamar da aikin layin dogo na Sin-Kyrgyzstan-Uzbekistan a birnin Jalal-Abad dake Kyrgyzstan, inda shugaban Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bikin.
A cikin sakonsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, gina layin dogo na Sin-Kyrgyzstan-Uzbekistan, wani muhimmin mataki ne da gwamnatocin kasashen uku suka dauka, da nufin yin cudanya da juna, da samar da wadata da kwanciyar hankali a shiyyar, kuma ana fatan hukumomi, da kamfanonin da abin ya shafa na kasashen uku za su yi hadin gwiwa tare, don inganta aikin gini mai inganci, da kokarin daga kimar layin dogon na Sin-Kyrgyzstan-Uzbekistan zuwa wani babban aiki dake karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ta yadda za a kara taimakawa ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al’umma, da inganta rayuwar jama’a a shiyyar bisa shawarar, da kuma ba da sabon kuzari wajen gina al’umma mai makomar bai daya ta daukacin al’ummun Sin da kasashen Asiya ta tsakiya. (Safiyah Ma)