A yau Jumma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga bikin baje kolin masana’antun samar da kayayyakin kirkirarriyar basira na kasa da kasa na shekarar 2025.
Cikin wasikarsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, fasahar kirkirarriyar basira ta AI tana bunkasa cikin sauri, tana kuma canja salon zaman rayuwar al’umma, da kuma yadda suke gudanar da ayyuka, tare da daidaita tsarin masana’antun kasashen duniya. Kasar Sin tana mai da matukar hankali kan rayawa da daidaita fasahar AI, yayin da kuma take zurfafa ayyuka a fannin kirkire-kirkiren fasahohin AI, da harkokin masana’antu cikin hadin gwiwa, domin kara bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da kyautata zaman rayuwar al’umma.
Xi, ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen duniya a aikin nazarin fasahar AI, da kuma mu’amala da kasashen duniya kan manufar raya fasahar AI, da tsarin gudanar da harkoki masu nasaba da hakan, da kuma daga matsayin fasaha da dai sauransu, ta yadda za a raya masana’antun samar da kayayyakin kirkirarriyar basira yadda ya kamata, da samar da sakamakon da zai tallafawa al’ummomin kasa da kasa.
A yau Jumma’a ne aka bude bikin baje kolin masana’antun samar da kayayyakin kirkirarriyar basira na kasa da kasa na shekarar 2025, a birnin Chongqing na kasar Sin. Babban taken biki na wannan karo shi ne “Fasahar AI+”, da “Hada fasahar AI cikin motoci masu aiki da wutar lantarki”. Kana, ana gudanar da bikin ne bisa hadin gwiwar gwamnatin birnin Chongqing da gwamnatin birnin Tianjin. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp