Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga kwamitin kasa na shirya liyafar karrama gwaraza a fannin raya alakar Sin da Amurka na shekarar nan ta 2024.
A jiya Talata ne dai shugaba Xi ya aike da wasikar, wadda a cikin ta ya jinjinawa kwazon kwamitin a fannin bunkasa musaya, da hadin gwiwa a fannoni daban daban tsakanin Sin da Amurka.
- Gidauniyar Sam Nda-Isaiah Ta Miƙa Miliyan 250 Da Gwamna Bago Ya Ba Ɗan Adaidaita Sahun Kano
- Ba Zan Ce Komai Game Da Rikicin NNPP Ba – Kwankwaso
Shugaba Xi, ya ce alakar Sin da Amurka na cikin mafiya muhimmanci tsakanin wasu kasashe biyu na duniya. A bangaren ta kasar Sin na nacewa gudanar da wannan alaka bisa la’akari da ka’idojin martaba juna, da zaman lafiya, da hadin gwiwar cimma moriyar juna, kuma har kullum tana da imanin cewa nasarar sassan biyu dama ce ta bai daya gare su.
Xi ya kuma jaddada cewa, Sin za ta kara fadada kwazon ta wajen bude kofa ga hukumomin juna, da kara gina kyakkyawan yanayin kasa da kasa don raya cudanyar kasuwanci a matakin koli. Kaza lika, za ta yi amfani da fifikon babbar kasuwarta, da bukatun cikin gida, wajen gabatar da karin damammakin raya hadin gwiwar ta da Amurka.
Daga nan sai ya yi fatan kwamitin na kasa, da sauran kawayen Sin daga dukkanin fannonin rayuwa, za su ci gaba da mayar da hankali, da goyon bayan alakar Sin da Amurka, tare da ci gaba da shiga a dama da su, a ayyukan zamanantarwa irin ta Sin, da cin gajiya daga hakan, da gabatar da alheran dake tattare da hakan ga al’ummun su, da ingiza karin daidaito, da karsashi cikin harkokin kasa da kasa.
Har ila yau, a dai jiyan, shi ma shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya aike da sakon sa na taya murna ga kwamitin kasa mai shirya liyafar karrama gwaraza duk shekara, a fannin raya alakar Sin da Amurka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)