A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron fahimtar kasar Sin na 2024, wanda ya gudana a birnin Guangzhou, na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.
Xi ya bayyana cewa, don fahimtar kasar Sin, ana bukatar fahimtar yadda za a kara zurfafa yin gyare-gyare da yayata aikin zamanintarwa mai salon kasar Sin. Kana yunkurin zamanintarwa mai salon kasar Sin ba wai kawai zai cimma muradun mutane biliyan 1.4 na samun ingantacciyar rayuwa ba, har ma zai bayar da sabuwar gudumawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya.
Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin aiki tare da sauran kasashen duniya wajen samar da muhalli da yanayin da suka dace da samun ci gaba, da tinkarar matsaloli da kalubale daban-daban, da sa kaimi ga zamanintar da dukkan kasashen duniya tare da samun bunkasuwa cikin lumana, da hadin gwiwar moriyar juna, da samun wadata tare, da rubuta sabon babi na gina al’umma mai makoma bai daya ga bil Adama. (Mohammed Yahaya)