Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron kasa karo na tara na kungiyar yara jagorori na kasar Sin (CYP), wanda aka bude a yau Talata a birnin Beijing.
Xi ya jaddada muhimmancin ganin kungiyar ta bi sawun jam’iyyr kwaminis ta kasar Sin a da kuma yaye hazikai masu gina kasa da za su raya hanyar gurguzu mai sigogin kasar Sin.
A game da bikin ranar yara ta duniya da za a yi a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, ya taya musu shiryawa murna a madadin kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ya mika sakon gaisuwa ga dimbin yara jagororin, da masu dora su a kan hanya, da bangarensu na ma’aikata, tare da fatan alheri da taya murna ga daukacin yara na fadin kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)












