A kwanakin nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da Matias Tarnopolsky, shugaban kungiyar kade-kade ta Philadelphia dake kasar Amurka ya rubuta masa.
A cikin wasikar shugaba Xi Jinping ya ce, ya yi matukar farin ciki da samun labarin cewa, kungiyar kade-kaden ta Philadelphia ta zo kasar Sin karo na 13 a watan Nuwamba, tare da yin hadin gwiwa da bangaren kasar Sin, wajen gudanar da jerin ayyukan mu’amala, domin tunawa da ziyarar farko da ta kawo kasar Sin a shekarar 1973.
- Gwamna Radda Ya Yi Allah Wadai Da Hare-haren ‘Yan Fashin Daji A Jihar Katsina
- Halin Da Ake Ciki Bayan Wata Hudu Da Juyin Mulkin Nijar
Shekaru hamsin da suka gabata, kungiyar makadan ta zo kasar Sin don fara “rangadin kulla zumunta” kan mu’amalar al’adu tsakanin Sin da Amurka, wanda ke da matukar muhimmanci wajen daidaita alakar dake tsakansin kasashen Sin da Amurka.
A cikin shekaru 50 da suka wuce, kungiyar kade-kade ta ziyarci kasar Sin har sau 12 a matsayin “jakadan al’adu” tsakanin kasashen Sin da Amurka, tare da taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka. Ya jaddada cewa, waka ta wuce iyakokin kasa. Ya yi fatan kungiyar kade-kade ta Philadelphia da masu fasaha daga ko’ina a duniya, ciki har da kasashen Sin da Amurka, za su ci gaba da bude wani sabon babi na mu’amalar al’adu da abokantaka tsakanin Sin da Amurka da jama’ar dukkan kasashe.
A watan Satumban shekarar 1973, kungiyar kade-kade ta Philadelphia ta kawo ziyarar farko a kasar Sin, inda ta zama kungiyar makada ta Amurka ta farko da ta ziyarci kasar Sin bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. (Mai fassara: Ibrahim)