A kwanakin nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wata wasika da wakilan masu fasaha na Larabawa da suka ziyarci kasar Sin, don halartar bikin baje kolin “Kayayyakin fasaha a hanyar siliki” suka rubuta masa, inda ya karfafa musu gwiwa da su kara bijiro da wasu fasahohin da ke nuna abokantakar dake tsakanin Sin da Larabawa, da ba da sabbin gudummawa ga abokantakar dake tsakanin al’ummomin kasashen biyu. (Mai fassarawa: Ibrahim)