Kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da wakilan daliban da suka halarci babbar gasar kere-keren kimiyya ta daliban jami’o’in kasa da kasa ta kasar Sin suka aika masa, inda ya kara karfafa musu gwiwa, tare da yi musu kyakkyawan fata.
A cikin wasikar, shugaba Xi ya yi fatan daliban da suka halarci gasar za su yada ruhin kimiyya da kuma nuna kwazo da himma kan nazarin kere-keren kimiyya da fasaha, ta yadda za su ba da gudummowarsu kan ingiza ci gaban kimiyya da cudanyar kimiyya da fasaha tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya.
Gaba daya babbar gasar kere-keren kimiyya ta kasa da kasa da kasar Sin ta shirya a bana, ta samu halartar daliban jami’o’i sama da miliyan 20 da suka fito daga kasashe da yankuna 153 dake fadin duniya. Kwanan baya wakilan daliban 25 sun rubuta wata wasika zuwa ga shugaba Xi, inda suka bayyana anniyarsu ta yin aiki tukuru kan kere-keren kimiyya domin sauke nauyin dake wuyansu a sabon zamani. (Mai fassara: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp