Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a hada hannu wajen gina shawarar ziri daya da hanya daya wato BRI a takaice domin bude kofofin sabbin damarmaki ga dangantakar Asiya da Turai.
Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen bikin bude taron dandalin tattauna tattalin arziki na Turai da Asiya karo na biyu na kungiyar raya tattalin arzikin Turai da Asiya.
Cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, shugaba Xi ya ce duniya na fuskantar manyan sauye-sauyen da aka dade ba a gani ba, kuma yanayin dangantakar bangarori daban-daban da dunkulewar tattalin arzikin duniya, abubuwa ne da ba za a iya gujewa ba, yana mai cewa, ita ce matsayar da al’ummun kasa da kasa suka cimma, wato daukaka dangantakar kasa da kasa ta hakika da inganta ci gaba a fadin yankuna.
A cewarsa, yankin Turai da Asiya ne ke da jama’a mafi yawa a duniya, da kasashe mafi yawa da kuma al’adu mabanbanta. Ya ce a wannan zamani dake tattare da kalubale da sauye-sauye, raya dangantakar Asiya da Turai ba batu ne da ya shafi inganta rayuwar al’ummun yankin kadai ba, domin yana da muhimmin tasiri kan ci gaban duniya.
Shugaban na kasar Sin ya kuma gabatar da shawarar ci gaban duniya da ta tabbatar da tsaron duniya da ma ta wayewar kan duniya, yana mai kira ga dukkan kasashe su hada hannu tare wajen gina duniya mai kyau da ta kunshi kowa da kowa kuma mai tsafta da adalci da zaman lafiya mai dorewa da tsaro da ci gaba na bai daya tare da gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil Adama. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)