Sakatare janar na kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya bukaci a kara zage damtse wajen farfado da kauyuka domin daukaka aikin zamanantar da kasar Sin.
Xi Jinping ya bayyana haka ne jiya Talata, yayin rangadin da ya yi a birnin Xianning dake lardin Hubei na tsakiyar kasar Sin, inda ya ziyarci wata gonar kayan lambu da wani kauye.
- Sin Ta Yi Alkawarin Fadada Bude Kofa Da Hadin Gwiwa Da Kasa Da Kasa
- Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Lardin Hubei
Da yake bayyana ci gaba a matsayin abu mafi muhimmanci, ya ce ya kamata bunkasa kauyuka ya dogara da bunkasa sana’o’i, kuma mayar da hankali ga ayyukan gona ka iya samar da wadata, bisa la’akari da dimbin damarmaki dake akwai a bangaren.
Xi Jinping ya kuma nanata cewa, wajibi ne kwamitocin JKS da gwamnatoci a dukkan matakai su ba ayyukan da suka shafi gona da kauyuka da manoma muhimmanci, da karfafa tubalan ayyukan da inganta hidimomin bangarori, tare da tabbatar da samar da ingantacciyar rayuwa ga jama’a. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)