Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar ci gaba da daukakawa da inganta tsarin tafiyar da majalisar wakilan jama’ar kasar, wanda shi ne kashin bayan tsarin siyasar kasar, yadda ya kamata. Shugaban ya bayyana haka ne yayin wani taro a yau Asabar, domin murnar cikar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin shekaru 70 da kafuwa.
Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban kwamitin koli na sojin kasar, ya nanata bukatar kara kwarin gwiwa kan hanya da tunani da tsari da al’adun gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp