Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci a kara zurfafa aikin farfado da kauyuka da samun ci gaba mai kwari wajen cimma burin karfafa karfin kasar Sin a bangaren aikin gona.
Xi Jinping ya bayyana haka ne cikin umarnin da ya bayar kan ayyukan da suka shafi aikin gona da yankunan karkara da manoma, wanda aka nazarta yayin taron shekara-shekara kan ayyukan raya yankunan karkara, wanda ya gudana a birnin Beijing daga Talata zuwa yau Laraba.
A cewar shugaban, ya zama wajibi a inganta tsare-tsaren da za su taimaka wajen karfafa aikin gona da taimakawa manoma da wadata yankunan karkara da kuma daukaka aikin farfado da kauyuka ta kowacce fuska.
Ya ce, ya kamata a yi kokarin tabbatar da daidaito a fannin samar da hatsi da sauran muhimman amfanin gona da fadada nasarorin da aka samu na yaki da fatara da tabbatar da hannun agogo bai koma baya ba ta fuskar yaki da talauci. (Fa’iza Mustapha)