Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci a yi cikakkiyar kokarin karfafa aikin da ya shafi dabarun soja kan sabon tafarki a sabon zamani, da samar da tsarin dabarun soja na zamani mai halin musamman na kasar Sin.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja na kasar, ya bayyana hakan ne cikin umurninsa da aka sanar yayin wani taro kan aikin da ya shafi dabarun aikin soja, wanda aka gudanar daga ranar Litinin zuwa Talata a birnin Beijing. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp