Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci dakarun makami mai linzami na kasar da su karfafa dabarunsu na dakilewa da karfin yaki, da kuma dagewa wajen aiwatar da ayyukan da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jama’ar kasar suka dora musu.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya bayyana hakan ne yayin da yake duba wani birged daga dakarun makami mai linzami na rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin a ranar Alhamis. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp