Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga Sin da EU su samar da kwanciyar hankali da tabbaci ga duniya ta hanyar kyautata dangantakarsu.
Xi Jinping ya bayyana haka ne yau Alhamis, yayin ganawarsa da shugaban majalisar EU Antonio Costa da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen, wadanda suka zo Beijing domin halartar taro na 25 na Sin da EU.
- Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati
- Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
A cewar shugaban, a bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da EU, da kuma cika shekaru 80 da kafuwar MDD, yana cewa dangantakar Sin da EU ta shiga wani muhimmin mataki a tarihi.
Ya ce cikin shekaru 50 da suka gabata, Sin da EU sun cimma kyawawan sakamakon musaya da hadin gwiwa wadanda suka haifar da nasarori ga bangarorin biyu da dimbin alfanu ga duniya.
Har ila yau, ya ce yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauyen da hargitsin da ba a taba gani ba, ya kamata shugabannin Sin da EU su kara yin hangen nesa da yin kyakkyawan zabin da ya dace da abun da jama’a ke sa ran gani su kuma jure yanayin da tarihi ya zo da shi. (Mai fassara: Fa’iza Mustpha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp