Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga al’ummar kasar da su kara yakini da yin kokarin hadin kai a kokarin da suke yi na gina kasar Sin mai karfi da kuma cimma nasarar farfado da kasar.
Xi Jinping, ya ce, karfinmu ya samo asali ne daga hadin kai, kuma kwarin gwiwa ya fi zinari daraja, Xi ya fada haka ne a wata gagarumar liyafar da aka yi a nan birnin Beijing, domin murnar cika shekaru 74 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.
Xi ya kara da cewa, makoma na da haske, kuma ya kamata al’ummar kasar su ci gaba da shawo kan wahalhalu da kuma ci gaba da tafiya (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp