Babban sakataren JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci babban taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin JKS da jam’iyyun siyasa na duniya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.
Xi ya jaddada cewa, a daidai lokacin da makomar kasashen duniya ke da alakar kut-da-kut da juna, al’ummomi daban-daban na iya kasancewa tare, kana musayar al’adu daban-daban na taka muhimmiyar rawa wajen inganta zamanantar da daukacin bil-Adama.
Ya ce, “A nan, ina so in gabatar da shawarar wayewar kai ta duniya. Ya kamata mu hada kai mu ba da shawarar mutunta bambantan wayewar kai ta duniya tare da martaba daidaito, koyi da juna, da tattaunawa, da hakuri a tsakanin mabambanta wayewar kai. Ya kamata mu ba da shawarwari tare da aiwatar da kyawawan dabi’u na dukkan bil-Adama. Zaman lafiya, ci gaba, daidaito, adalci, demokuradiyya, da ‘yanci, su ne abin da jama’ar kasashen duniya ke bi na bai daya. Ya kamata mu fahimci wayewar kai daban-daban game da ma’anar dabi’u tare da zurfin tunani, kuma bai kamata mu dora dabi’u wasu zama abin koyi a kan wasu ba, kuma bai dace mu shiga fadace-fadace na akida ba.”
Xi ya jaddada cewa, babban burin zamanantar da jama’a shi ne samun ci gaban jama’a cikin ‘yanci da inganci. Zamantakewa ba alama ce ta wasu kasashe ba, kuma wani ne ya zaba ba. A lokacin da kasa za ta koma ga tsari na zamani, bai kamata ta rika bin ka’idojin zamani na zamani kadai ba, har ma ta dogara da yanayin kasa. A shirye JKS take wajen zurfafa mu’amala da jam’iyyu da kungiyoyin siyasa na kasashe daban-daban, da kuma fadada hadin kan ra’ayoyi da muradu daga lokaci zuwa lokaci, ta yadda za a kafa wani sabon nau’in dangantakar jam’iyyun siyasa, da taimakawa wajen gina sabon nau’in hadin gwiwar kasa da kasa.
An gudanar da babban taron tattaunawa tsakanin JKS da jam’iyyun siyasa na duniya ta kafar bidiyo. Taken tattaunawar dai shi ne “Tafarkin zamanantarwa: Nauyin dake wuyan jam’iyyun siyasa.” (Mai fassarawa: Ibrahim)