Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar gudanarwar Turai Charles Michel da shugabar kungiyar tarayyar kasashen Turai Ursula von der Leyen a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.Shugabannin sun zo kasar Sin ne domin halartar taron ganawar shugabannin Sin da Turai karo na 24.
Xi Jinping ya ce, tun karshen shekarar 2022 zuwa yanzu, kasar Sin da kasashen Turai sun cimma sakamako da dama bisa shawarwarin da aka yi tsakanin manyan jami’an bangarorin biyu kan fannonin manyan tsare-tsare, da tattalin arziki da cinikayya, da kiyaye muhalli da fasahar sadarwa ta yanar gizo da sauransu. Dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu na bunkasa kamar yadda ake fata, lamarin da ya dace da moriyar kasashen biyu da ma fatan al’umma.
Xi ya yi nuni da cewa, duniya a yau tana fuskantar manyan sauye-sauye da ba a taba ganin irinta ba cikin karni, kuma dangantakar dake tsakanin Sin da Turai na da nasaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a duniya. Kasar Sin da kasashen Turai suna da alhakin samar da karin kwanciyar hankali a duniya tare, da samar da karin kuzari ga ci gaba, da ba da jagoranci da goyon baya ga harkokin tafiyar da harkokin duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)