Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Indonesia Prabowo Subianto a yau Asabar a birnin Beijing, inda Xi ya bayyana cewa, riko da cin gashi kai bisa manyan tsare-tsare, da amincewa da juna, da taimakon juna, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna, da samun daidaito da adalci, ba kawai sun kasance takaitaccen tarihin bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Indonesia a cikin shekaru da dama da suka gabata ba, har ma sun kasance wani muhimmiyar ka’ida da ya kamata a bi cikin dogon lokaci don samun ci gaban dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a nan gaba.
Xi ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sabuwar gwamnatin Indonesia, wajen gina al’umma mai makomar bai daya mai ma’ana da tasiri a shiyya da ma duniya baki daya, da kuma rubuta wani sabon babi na yin hadin kai, da mara wa juna baya, da yin hadin gwiwa don samun moriyar juna da samun nasara tare a tsakanin manyan kasashe masu tasowa. (Yahaya)