Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugabar kasar Mexico, Claudia Sheinbaum Pardo, da shugaban kasar Chile, Jose Antonio Kast, da kuma shugabar kasar Peru, Keiko Fujimori, a birnin Shenzhen, yau Talata.
A yayin ganawarsa da shugabar kasar Mexico, Xi ya jaddada cewa ya kamata Sin da Mexico su yi mu’amala da juna cikin gaskiya da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da neman cin moriyar juna da kuma samun nasara ga kowane bangare domin daukaka hadin gwiwa ta abota, da yin riko da adalci da kuma karfafa tsarin mabambantan bangarori na duniya, kana da gina kyakkyawar makoma ta bai-daya don zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Latin Amurka.
A ganawarsa da shugaban kasar Chile kuwa, Xi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Chile su ci gaba da goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi manyan muradun juna da kuma manyan abubuwa masu ci musu tuwo a kwarya. Bangarorin biyu, za su ciyar da dadadden hadin gwiwarsu gaba tare da binciko sabbin fannoni masu tasowa, ciki har da fasahar kirkirarriyar basira, da binciken kimiyya na yankunan duniya, da kuma binciken teku mai zurfi. Kazalika ya ce, kasar Sin a shirye take ta kara inganta tuntubar juna da hadin gwiwa da kasar Chile a cikin tsarin mabambantan bangarori na duniya kamar APEC, domin hada hannu wajen yin riko da tsarin mabambantan bangarorin na duniya.
Yayin da yake ganawa da shugabar kasar Peru kuma, shugaba Xi ya yi nuni da cewa ya kamata Sin da Peru su ci gaba da mu’amalar sada zumunci da karfafa tuntubar juna a dukkan matakai da kuma fannoni daban-daban.
Bangarorin biyu za su karfafa tsarin mu’amalarsu bisa manyan tsare-tsare, da cikakken bude cin gajiyar dukkan fa’idodin da yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci da aka daga darajarta tsakanin Sin da Peru ta samar, da kuma cimma samun wadata tare. Haka nan, bangarorin biyu za su fadada musaya da cudanyar al’ummominsu a bangaren al’adu, da ilimi, da yawon bude ido, da binciken kayan tarihi da kuma kiwon lafiyar jama’a.
Kasashen biyu za su kuma karfafa tsarin mabambantan bangarori na duniya domin kiyaye hakikanin tsarin mabambantan bangarori da kuma cinikayya cikin ‘yanci. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














