Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, a yau Litinin, ya halarci bikin maraba da babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam To Lam ya shirya masa, a birnin Hanoi na kasar Vietnam.
Daga bisani shugabannin biyu sun yi tattaunawa a hedikwatar kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Vietnam.
Kana shugaba Xi ya kuma gana da firaministan kasar Vietnam Pham Minh Chinh da shugaban majalissar dokokin kasar Tran Thanh Man daya bayan daya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)