A ranar 16 ga wannan wata agogon kasar Peru, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa cibiyar taro ta Lima domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC karo na 31, tare da gabatar da wani muhimmin jawabi.
Cikin jawabinsa, Xi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, ana yin manyan sauye-sauye a duk fadin duniya, domin tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, kuma an gamu da matsala yayin bude kofa ga wasu, sannan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik shi ma yana fama da kalubale.
- Gwamnatin Bauchi Ta Kaddamar Da Kwamitin Adana Kayan Abinci
- An Yi Bikin Kaddamar Da Shirin Zababbun Kalaman Shugaba Xi Jinping “Zango Na 3” Da Harshen Sifaniya A Peru
A don haka shugaban ya ce, ya dace kasashen yankin su hada kai domin tabbatar da muradun Putrajaya nan da shekarar 2040 da shugabannin APEC suka fitar a shekarar 2020, da karfafa gina kyakkyawar makomar bai daya ta al’ummun kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik, tare kuma da kafa sabon zamani na ci gaban yankin.
Daga baya shugaba Xi ya gabatar da shawarwari uku, na farko, kafa tsarin hadin gwiwa ba tare da rufa-rufa ba tsakanin kasashen yankin. Ya ce, kasar Sin tana nacewa kan manufar aiwatar da tsare-tsaren RCEP, da CPTPP, da DEPA, haka nan tana son tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa kan cinikayya a fannonin fasahar zamani da kare muhalli, tare kuma da kara habaka yankunan cinikayya marasa shinge zuwa matakin koli a fadin duniya.
Na biyu, neman samun sabon kuzarin kere-kere a yankin Asiya da tekun Fasifik, inda kasar Sin za ta fitar da “Shawarar hadin gwiwa kan musayar alkaluma tsakanin kasashen duniya”, domin zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya a bangaren.
Na uku, tsara tunanin raya yankin Asiya da tekun Fasifik da zai haifar da alfanu ga kowa da kowa, yayin da a nata bangaren, kasar Sin za ta yi kokari domin kara kudin shigar al’ummun kasashen mambobin kungiyar APEC, da daukaka ci gaban matsakaita da kananan masana’antu, da habaka ci gaban tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasifik.
Ban da wannan kuma, Xi ya sanar da cewa, kasar Sin ce za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron da shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta yankin Asiya da teku Fasifik APEC za su gudanar a shekarar 2026. Ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da kuma tsumayar aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa wajen zurfafa hadin gwiwar yankin Asiya da tekun Fasifik domin amfanar da al’ummomin manyan yankunan guda biyu. (Mai fassara: Jamila)