• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Halarci Liyafar Maraba Da Shugaban Faransa Ya Shirya

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Xi Ya Halarci Liyafar Maraba Da Shugaban Faransa Ya Shirya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar maraba da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya shirya a ranar 6 ga watan Mayu a agogon Faransa, inda ya gabatar da jawabi.

  • Xi Ya Yi Tsokaci Kan Hargitsin Palastinu Da Isra’ila Da Rikicin Ukraine

A cikin jawabinsa, Xi ya bayyana cewa, Sin da Faransa abokai ne na musamman, kuma dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa dangantaka ce ta musamman tsakanin manyan kasashen duniya. Ta kasance ta musamman saboda kasashen biyu suna riko da ruhin ‘yancin kai.

Xi ya ce, bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Faransa. Shekaru 60 sun shude, duk da sauye-sauyen da ake samu a yanayin kasa da kasa, shugabannin kasashen Sin da Faransa na zamanin da suka gabata sun nazarci da kuma tafiyar da wannan dangantaka da dabarun hangen nesa kuma na dogon lokaci.

Dangantakar Sin da Faransa ta musamman ce ta yadda suke fahimtar juna, a cewar Xi, ya kara da cewa, an kebe wannan shekarar a matsayin shekarar al’adu da yawon bude ido ta Sin da Faransa. Kasashen biyu za su iya amfani da shi a matsayin wata dama na kara fahimtar al’adun juna.
Xi ya kuma ci gaba da cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa na da muhimmanci, domin dukkansu na sauke nauyin dake wuyansu. Duniyarmu a yau tana fuskantar sauye-sauye da tashin hankali. Kasancewarsu mambobi na dindindin na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, Sin da Faransa suna da alhakin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. Kasar Sin da Faransa sun amince da kara zurfafa amincewa da hadin gwiwa a tsakaninsu, da karfafa tuntubar juna da yin hadin gwiwa kan manyan batutuwan kasa da kasa, tare da ingiza fata a duniya mai cike da rudani da gano hanyar samun ci gaban bil’Adama. (Mai fassara: Yahaya)

Labarai Masu Nasaba

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Bunkasa Tattalin ArzikiliyafaXi Jinping
ShareTweetSendShare
Previous Post

Xi Ya Yi Tsokaci Kan Hargitsin Palastinu Da Isra’ila Da Rikicin Ukraine

Next Post

Xi Ya Halarci Bikin Rufe Taron Kwamitin ‘Yan Kasuwan Sin Da Faransa Karo Na 6

Related

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana
Daga Birnin Sin

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

13 minutes ago
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5
Daga Birnin Sin

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

1 hour ago
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu
Daga Birnin Sin

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

2 hours ago
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani
Daga Birnin Sin

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

3 hours ago
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
Daga Birnin Sin

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

22 hours ago
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

23 hours ago
Next Post
Xi Ya Halarci Bikin Rufe Taron Kwamitin ‘Yan Kasuwan Sin Da Faransa Karo Na 6

Xi Ya Halarci Bikin Rufe Taron Kwamitin ‘Yan Kasuwan Sin Da Faransa Karo Na 6

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

July 27, 2025
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

July 27, 2025
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

July 27, 2025
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

July 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Sojojin Bogi 2 A Legas

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yanbindiga Uku Da Kama AK-47 Guda Goma

July 27, 2025
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

July 27, 2025
Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

July 27, 2025
Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

July 27, 2025
ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

July 27, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.