Babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a yau Laraba, game da cika shekaru 70 da kafuwar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai, a wata cibiyar raya al’adu dake birnin Urumqi, fadar mulkin jihar.
Bikin nune-nunen ya samar da bayanai masu fadi, dangane da ci gaban da aka cimma sakamakon dunkulewa, da jajircewa, da kwazon al’ummun mabanbantan kabilun jihar ta Xinjiang cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, karkashin kakkarfan jagorancin JKS, da goyon baya mai tasirin gaske daga sauran sassan kasar ta Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














