An yi babban taron kare muhallin halittu na kasar Sin a ranakun 17 da 18 ga wata, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimman matakai da kasar za ta dauka, don cimma burin gina kyakkyawar kasar Sin daga dukkan fannoni.
A cikin shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta mai da aikin kiyaye muhallin halittu a matsayin babbar manufar neman samun dauwamammen ci gaban al’ummar Sinawa, inda ta gudanar da jerin ayyukan da ba a taba gudanarwa a baya ba. Manyan sakamakon da aka aka samu kuwa sun taimakawa sosai, wajen gina kyakkyawar kasar Sin daga dukkan fannoni.
A yayin wannan babban taron, Shugaba Xi ya gabatar da matakai game da yadda za a hanzarta ci gaban zamanantarwa ta hanyar kiyaye muhallin halittu, da rage yawan iskar Carbon da aka fitar. Hakan ya shaida cewa, Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai mulkin kasar na kokarin tsimin makamashi, da kare muhalli, yayin da take jagorantar al’ummar kasar wajen raya zamanantarwar kasar.
Burin zamanantar da kasar Sin da ake kokarin cimmawa, ya sha bamban da yadda kasashen yammacin duniya suka samu zamanantarwa, wato kasar Sin ta bar hanyar gargajiya ta raya ayyukan masana’antu ba tare da yin la’akari da muhallin halittu ba, a maimakon haka, tana bin hanyar mayar da batun kare muhallin halittu a gaban komai, yayin da ake raya masana’antu, a kokarin samun ci gaban zamanantarwa mai kunshe da zaman jituwa tsakanin bil-Adama da muhallin sa. (Kande Gao)