A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin raya cikakken tsarin hadin gwiwa mai inganci karkashin shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne sakataren koli na JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi wannan tsokaci ne a cikin jawabinsa, yayin wani taron karawa juna sani game da bunkasa shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI.
- Kananan Manoma Mata Sun Bukaci Kara Yawan Kasafin Kudin Aikin Noma
- Hukumar Gwamnati Mafi Ƙwazo A Shekarar 2024: Hukumar Ilimin Bai-ɗaya (UBEC)
Xi ya ce tun bayan gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya a shekarar 2013, karkashin kwazon dukkanin sassa, shawarar ta ci gaba da gudana kafada da kafada da ruhin hanyar siliki, na raya hadin gwiwa cikin lumana, da yin komai a bude game da dukkanin sassa, da koyi da juna, da cimma gajiyar nasarar kowa da kowa. Kaza lika, kamar ko da yaushe, tana nacewa ka’idojin tuntubar juna, da ginawa da raba riba tare.
Bugu da kari, an ci gaba da fadada hadin gwiwa, yayin da matsayin hadin gwiwa ke ci gaba da kyautata. Ana kara janyo hankulan sassan kasa da kasa, tasiri da daidaito sun ci gaba da inganta, yayin da Sin ke bayar da gudummawarta, wajen sake gina kawance da kasashen dake cikin shawarar, da ingiza bunkasar tattalin arziki, da zamantakewa a fannin kara gina kasashe. (Mai fassara: Saminu Alhassan)