A yayin ziyararsa da farko tun bayan kammala babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) na 20, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara kaimi ga aikin farfado da yankunan kasar baki daya, da kara azama wajen ganin an cimma burin zamanantar da aikin gona da na yankunan karkara da aka sanya a gaba.
Ya bayyana a yayin da ya ziyarci Yan’an dake lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar da birnin Anyang dake yankin tsakiyar kasar daga ranar Laraba zuwa Jumma’a cewa, ya zama tilas a ba da muhimmanci wajen raya yankunan karkara, da kara fadada nasarorin da kasar ta cimma wajen kawar da kangin fatara.
Bisa nasarar da kasar ta cimma a fannin kawar da talauci, yanzu haka a shirye kasar ta ke ta sake yin wani sabon zagaye na raya aikin gona da yankunan karkara, a gabar da ake ci gaba da kara himma wajen ciyar da yankunan kasar gaba yadda ya kamata.
Rahoton da aka gabatarwa babban taron wakilin JKS karo na 20,ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da sanya batun raya aikin gona da yankunan karara a gaba, da kara kaimi da fadada nasarorin da aka cimma wajen yakar fatara, da karfafa tushen samar da abinci daga dukkan fannoni. (Ibrahim)