Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara samar da kwararrun jami’ai masu aminci, da gaskiya, da sanin ya kamata, ga jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya bayyana hakan ne a cikin wani umarni na baya-bayan nan, wanda ya karanta a taron karawa juna sani da aka gudanar a ranar Asabar, don murnar cika shekaru 70 da kaddamar da shirin horar da jami’ai ‘yan kananan kabilu na Xinjiang a cikin makarantar horas da manyan jami’an JKS. (Yahaya)