Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jadadda “rubuta wani sabon babi” na kokarin sake farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin, yayin da ya kira wani muhimmin taro a lardin Heilongjiang a wannan mako.
Xi ya bayyana hakan ne a wajen taron da aka gudanar a Harbin babban birnin lardin a yammacin ranar Alhamis.
Shugaban ya yi kira da a kara ba da taimako da karfafa kai don farfado da arewa maso gabashin kasar Sin a sabon zamani,. Ya kuma jadadda bukatar samar da wata hanya ta samun ci gaba mai inganci da kuma dorewa tare da karin jajircewa da ayyuka na zahiri. (Yahaya)