A yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon jaje ga takwaransa na Rasha Vladimir Putin, don gane da mummunan harin ta’addanci da ya auku a wani dakin taron kade kade dake yankin Moscow Oblast, lamarin da ya sabbaba rasuwar mutane da dama.
Cikin sakon na sa, shugaba Xi ya ce “Na kadu matuka da jin aukuwar wannan mummunan harin ta’addanci, wanda ya faru a zauren nuna wasannin kade-kade a Moscow, wanda ya haifar da mummunar asarar rayuka. A madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, ina mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, da fatan samun sauki da wadanda suka jikkata. Sin na adawa da duk wasu nau’ikan ayyukan ta’addanci, tana kuma Allah wadai da harin ‘yan ta’adda, kana tana goyon bayan kokarin gwamnatin kasar Rasha na wanzar da tsaron kasa da samar da daidaito”. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp