A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar taron koli na BRICS karo na 15 da zai gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, tare da kai ziyarar aiki a Afirka ta Kudu.
Xi ya kai ziyarar ce bisa gayyatar da takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi masa. Yayin da suke Afirka ta Kudu, shugabannin biyu za su jagoranci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da Afirka. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp