Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin JKS(Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin), ya karfafawa ‘ya’yan wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimtawa kasa, da su bi sawun iyayensu, bisa jarumtar da suka nuna a zamaninsu, tare da jajircewa wajen zama amintattu masu kare jam’iyyar da ma al’umma.
Shugaba Xi ya yi kiran ne a amsarsa ga wasikar da yara 8 wadanda yanzu haka ke karatu a jami’ar koyon harkokin tsaron jama’a ta kasar Sin, wato People’s Public Security University of China, suka rubuta masa. (Fa’iza Mustapha)
Talla