• English
  • Business News
Saturday, August 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Babban Taron Intanet Na Duniya Na Bana A Wuzhen

by CGTN Hausa and Sulaiman
9 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Babban Taron Intanet Na Duniya Na Bana A Wuzhen
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga babban taron intanet na duniya na bana da ake yi a garin Wuzhen ta hanyar bidiyo. 

Xi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, sabon zagaye na juyin-juya-halin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen masana’antu na samun bunkasa cikin sauri, kuma ana samun sabbin fasahohi irin su fasahar kirkirarriyar basira, wadanda suka kara inganta karfin fahimtar dan Adam da sauya fasalin duniya, ko da yake lamarin ya kuma zo da kasada da sauran kalubalen da ba a zata ba.

  • Sin Tana Fatan Raya Duniya Mai Adalci Dake Samun Bunkasuwa Tare Tsakanin Mabambantan Bangarori
  • An Kaddamar Da Bikin Kafofin Watsa Labaru Kan Raya Harkokin Matasan Kasashe Masu Tasowa A Birnin Rio de Janeiro

Shugaba Xi ya ce ya kamata a fahimci yanayin fasahar zamani gaba daya, da hanyoyin sadarwa da ci gaban fasaha, da daukar sabbin kirkire-kirkire a matsayin karfin gudanarwa na farko, sannan tsaro a matsayin ginshiki, da ci gaba mai hadaka a zaman neman mutuntawa, kana a habaka bullo da sabbin abubuwa cikin hanzari, da samar da aminci a harkokin intanet da kuma yin aiki tare don samar da kyakkyawar makoma ta fasahar zamani.

Labarai Masu Nasaba

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

Shugaban ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashe, wajen daukar mataki da zai kafa tarihi a bangaren juyin-juya-halin fasahar sadarwa, da gina al’umma mai makoma mai kyau a bangaren harkokin intanet da kuma sanya intanet din ya zama mai amfani ga jama’a da duniya baki daya.

An bude babban taro na duniya a kan intanet na shekarar 2024 na Wuzhen, a wannan ranar ce a garin Wuzhen dake birnin Tongxiang na lardin Zhejiang, mai taken “Rungumar kyakkyawar makomar dan Adam ta fasahar zamani mai kaifin basira-aiki tare don gina al’umma mai makoma mai kyau a bangaren harkokin intanet. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Shugabannin Kasashen Faransa Da Jamus Da Argentina A Gefen Taron Kolin G20

Next Post

Matatar Dangote Ta Fara Fitar Man Fetur Dinta Zuwa Kasashen Afrika

Related

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure
Daga Birnin Sin

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

54 minutes ago
Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”
Daga Birnin Sin

Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

2 hours ago
CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD

3 hours ago
Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani
Daga Birnin Sin

Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

4 hours ago
Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli
Daga Birnin Sin

Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli

5 hours ago
Kuri’ar Jin Ra’ayi Ta CGTN: Ya Kamata Japan Ta Martaba Tarihi
Daga Birnin Sin

Kuri’ar Jin Ra’ayi Ta CGTN: Ya Kamata Japan Ta Martaba Tarihi

6 hours ago
Next Post
Yaki A Hukumance Da Matatar Dangote Da `Yan Nijeriya

Matatar Dangote Ta Fara Fitar Man Fetur Dinta Zuwa Kasashen Afrika

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

August 15, 2025
An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jam’iyyar ADC Kan Shugabancin David Mark

An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jam’iyyar ADC Kan Shugabancin David Mark

August 15, 2025
Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

August 15, 2025
Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa

Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa

August 15, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD

CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD

August 15, 2025
Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

August 15, 2025
Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

August 15, 2025
Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

August 15, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

August 15, 2025
Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli

Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli

August 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.