Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron bunkasa ilmin sana’a da fasaha na kasa da kasa.
A cikin wasikar tasa, Xi ya yi nuni da cewa, koyar da sana’o’in dogaro da kai na da nasaba sosai da raya tattalin arziki da zamantakewa, kuma yana da muhimmanci matuka wajen inganta ayyukan yi da kasuwanci, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewa, da ma kyautata jin dadin jama’a.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana ingiza bunkasuwar koyar da sana’o’in dogaro da kai mai inganci, kuma tana goyon bayan yin mu’amala da hadin gwiwa da sauran kasashe.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shirye bangaren kasar Sin yake wajen yin aiki tare da sauran kasashe a duniya, don karfafa yin koyi da juna, da bayar da gudummawar hadin gwiwa, da cin moriya tare, da hada hannu wajen aiwatar da shirin raya duniya, da ba da gudummawa wajen gaggauta aiwatar da ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030. (Ibrahim)