Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Laraba, ya aike da sakon taya murna ga John Dramani Mahama bisa zabarsa da aka yi a matsayin shugaban kasar Ghana.
Xi ya bayyana cewa, kasar Ghana na daya daga cikin kasashen farko dake kudu da hamadar Sahara da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin, kuma muhimmiyar abokiyar hulda ce ta kasar Sin a Afirka, yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Ghana na da dadadden tarihi, kuma an dada karfafata a tsawon lokaci.
Har ila yau, a cikin sakon, Xi ya ce, yana dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Ghana, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da zababben shugaban kasar Mahama, wajen ci gaba da sada dadadden zumuncin, da zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da sa kaimi ga zurfafa da karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Ghana, ta yadda za a samar da karin moriya ga jama’ar kasashen biyu. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp