Shugaban hukumar koli ta aikin soji ta kasar Sin Xi Jinping, ya rattaba hannu kan umarnin amfani da wani jerin ka’idojin kare muhalli a bangaren aikin soji.
Ka’idojin sun fayyace manufofi da ayyukan kare muhalli a bangaren aikin soji kamar yadda manufofi da ka’idojin kasar suka tanada, tare da yin cikakken bayani game da bukatun da ake da su na kare muhalli a bangarorin da suka shafi ayyukan soji da sansanoni da kayayyakin aiki.
Talla
Ka’idojin da suka kunshi kasidu 50 cikin babuka 6, za su fara aiki ne a ranar 1 ga watan Oktoban 2024. (Fa’iza Mustapha)
Talla