Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo ga mahalarta taron sauyin yanayi na MDD, wanda ya gudana a birnin New York a jiya Laraba.
Cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya ce, a bana ake cika shekaru 10 da kulla yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, inda shekarar ta kasance wata muhimmiyar gaba da ta dace kasashen duniya su gabatar da kudurorinsu da za su zamo gudummawa ga cimma nasarar yarjejeniyar ko NDCs a takaice, kana lokaci ne da tsarin jagorancin sauyin yanayi ke shiga wani muhimmin mataki.
Daga nan sai shugaban na Sin ya gabatar da shawarwari uku, da suka hada da bukatar karfafa gwiwa domin tunkarar aikin da aka sanya gaba, da kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su sauke nauyin dake wuyansu, da jaddada muhimmancin zurfafa hadin gwiwa.
Shugaba Xi, ya sanar da sabbin kudurorin kasarsa da za su zamo gudummawa ga cimma nasarar yarjejeniyar Paris ko NDCs, wadanda suka hada da aniyar kasar Sin ta rage fitar da nau’o’in hayaki masu dumama yanayi, daga matsayinsu na koli zuwa tsakanin kaso bakwai zuwa kaso goma bisa dari nan zuwa shekarar 2035.
Kazalika, Sin za ta yi tsayin daka wajen kara kasonta na amfani da makamashi marar dumama yanayi, zuwa sama da kaso 30 bisa dari cikin jimillar makamashin da take konawa. Karkashin hakan, za ta kafa karin cibiyoyin samar da lantarki ta iska da hasken rana da yawansu zai ninka mizanin na shekarar 2020 sama da sau shida, inda ake sa ran karkashin wannan tsari a samar da jimillar da za ta kai gigawatt 3,600.
Sai kuma fannin fadada dazuzzuka da zai karu zuwa sama da kyubik mita biliyan 24, da mayar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi kan gaba, cikin jimillar ababen hawa da kasar za ta rika sayarwa, da fadada kasuwar carbon ta kasar Sin, ta yadda za ta game dukkanin manyan sassan fitar da hayakin carbon, tare da kafa al’umma mai ingancin rayuwa yayin da ake tunkarar sauyin yanayi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp