A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanya hannu kan umarnin shugaba na nada Li Qiang a matsayin firaministan kasar, a yayin taron majalisar dokokin kasar Sin da ya gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar.
Sabon firaministan kasar Sin Li Qiang da aka nada, ya yi alkawarin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar Asabar din nan.
A ranar Litinin da safe ne, ake saran Li zai gana da manema labarai a babban dakin taron jama’a, bayan kammala taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, kamar yadda cibiyar ‘yan jaridu ta bayyana a zaman farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp