Da yammacin yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci liyafar karramawa ga bakin da suka iso birnin Beijing daga sassan duniya daban daban, domin halartar taron koli na hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya karo na 3.
Shugaba Xi Jinping, ya yi jawabi a wajen bikin liyafar cewa, makasudin hadin gwiwar kasashe daban daban a karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, shi ne neman ci gaba, da amfana da juna, wanda hakan ke samar da damar bunkasuwa. Ya ce ydda ake yin hadin gwiwa karkashin shawarar cikin inganci, zai tabbatar da makoma mai haske ga daukacin bil Adama, bisa kokarin da dukkan kasashen da suka rungumi shawarar suke yi tare.
- Ganawa Da Xi Jinping: Ina Godiya Gare Shi Bisa Cimma Burina
- Sin Ta Kai Daukin Gaggawa Ga Falasdinawa
Taron na BRF dai zai gudana ne a ranaikun Talata da Laraba. Kuma jami’ai daga kasashe sama da 140, da wakilan hukumomin kasa da kasa sama da 30 sun tabbatar da halartar su. (Mai fassara: Saminu Alhassan)