Da yinin yau Alhamis 19 ga watan Yuni, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho, inda suka mai da hankali kan musayar ra’ayi game da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Putin ya bayyana ra’ayin Rasha game da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, ya kuma nuna aniyar kasar ta Rasha wajen ci gaba da magana da kasar Sin ba tare da jinkiri ba, kana da yin kokari tare wajen kwantar da hankula.
- An Kashe ‘Yan Ta’adda 6,260, An Ceto Mutane 5,365 Acikin Shekaru Biyu – Hedikwatar Tsaro
- Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
Xi Jinping ya yi karin haske kan matsayin kasar Sin kuma ya gabatar da shawarwari hudu kan halin da ake ciki yanzu.
Shawara ta farko ita ce, ya zama wajibi a karfafa tsagaita bude wuta da kuma dakatar da yakin. Kuma ya kamata bangarorin da ke rikici musamman Isra’ila, su tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba domin dakile bazuwar rikicin.
Ta biyu, a bai wa kare lafiyar fararen hula matukar fifiko. Sannan ya kamata bangarorin da ke rikicin su mutunta bin ka’idar dokokin kasa da kasa kuma su kaurace wa cutar da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
Shawara ta uka ita ce, hawa teburin tattaunawa da shawarwari ta zama babbar hanyar samar da mafita. Inda ya ce, dole ne mu yi tsayin daka wajen tabbatar babbar alkiblar da za a fuskanta kan warware matsalar nukiliyar Iran ta zama ta hanyar siyasa.
Ta hudu, ya bayyana cewa kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya abu ne mai matukar muhimmancin gaske. Kuma ya kamata kasashen duniya musamman ma manyan kasashen da ke da tasiri na musamman kan bangarorin da ke rikicin, su yi kokarin yayyafa ruwa amma ba akasin haka ba.
Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na son ci gaba da karfafa zantawa da gudanar da tsare-tsare da dukkan bangarorin, da kuma taka rawar da ta dace wajen maido da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp