• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Indonesia

byCMG Hausa
3 years ago
Xi

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Indonesia Joko Widodo da ke ziyara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi ya yi nuni da cewa, a karkashin jagorancin hadin gwiwarmu, dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia ta bunkasa cikin ‘yan shekarun nan, inda ta nuna juriya da kuzari.

  • Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Nace Kan Ra’ayin Hadin Gwiwa Na Hakika A Taron G20 A Indonesia

Bangarorin biyu sun karfafa amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare da zurfafa hadin gwiwar siyasa, da tattalin arziki, da al’adu da na harkokin teku.

Haka kuma, kasashen suna nuna irin nauyin da ke bisa wuyansu, tare da samun nasarori masu gamsarwa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da inganta nuna goyon baya da hadin gwiwa a duniya, da nuna kyakkyawan misali ga manyan kasashe masu tasowa, wajen neman karfi ta hanyar hadin kai da cin moriyar juna.

Shugaba Xi ya ce, ya kamata bangarorin biyu su zurfafa hadin gwiwa mai inganci game da shawarar “ziri daya da hanya daya” da samar da karin sakamako.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Xi ya yi nuni da cewa, sauye-sauyen da ake fuskanta a duniya, suna bulla ta hanyoyin da ba a taba ganin irinsu ba.

Don haka, ya kamata kasashen Sin da Indonesia, su yi aiki tare don nuna nauyin da ke bisa wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa, da aiwatar da ra’ayin bangarori daban-daban na zahiri, da kiyaye bude kofa ga kasashen waje, da ba da hikimomi na kasashen dake gabashin duniya, da ba da gudummawar karfin Asiya wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa.

A nasa jawabin kuwa, Joko Widodo ya bayyana cewa, kasashen Indonesia da Sin, abokan hulda ne bisa manyan tsare-tsare, kuma sun tsara muhimmin buri na gina al’umma mai makoma ta bai daya.

Hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, ta cin moriyar juna da samun nasara tare ce, wanda ba wai kawai tana kawo alfanu ga al’ummomin kasashen biyu ba, har ma tana bayar da muhimmiyar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a shiyyar da ma duniya baki daya.

Ya kara da cewa, kasar Indonesia tana son yin aiki tare da kasar Sin, don ci gaba da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya a yankin da ci gaban duk duniya.(Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Majalisa Ta Musanta Shirin Tsige Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila

Majalisa Ta Musanta Shirin Tsige Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila

LABARAI MASU NASABA

A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version