Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD FAO murnar cika shekaru 80 da kafuwa.
Cikin sakonsa na taya murnar, shugaba Xi ya ce FAO ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wadatar abinci a duniya, da inganta raya yankunan karkara da sauya tsare-tsaren samar da abinci da inganta rayuwar mutane a kasashe daban daban.
Xi Jinping ya jaddada cewa, gwamnatin Sin na daukar batun wadatar abinci da muhimmanci, kuma tana nace wa dogaro da kanta wajen samar da abinci ga mutane sama da biliyan 1.4, kuma ta samar da taimako iya karfinta ga kasashe mabukata, lamarin da ke bayar da gudunmowa ga samar da abinci a duniya.
Ya ce kamar ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da FAO ke takawa a bangaren aikin gona da samar da abinci a duniya.
An kafa hukumar FAO ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 1945, kuma Sin na daya daga cikin kasashe mambobi da suka kafa ta. (Fa’iza Mustapha)