Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Litinin ya aika da sakon taya murna ga Alassane Ouattara bisa sake lashe zabensa a matsayin shugaban kasar Cote d’Ivoire.
Xi ya nuna cewa, kasar Sin da Cote d’Ivoire abokan tafiya ne kuma abokan hulda nagari a kan hanyar zamanantarwa. Dangantaka tsakanin kasashen biyu na ci gaba da samun habaka mai kyau. Hadin gwiwa a fannoni daban daban ya samar da sakamako mai kyau, kuma zumunta a tsakanin mutanensu ta kara samun karbuwa a zukatan mutanen. A halin yanzu, sauye-sauyen da ake samu a duniya daga tsawon karni guda na karuwa cikin hanzari, kuma kasashe masu tasowa suna kara samun karfi. Ina dora fifiko kan raya dangantakar Sin da Cote d’Ivoire, kuma ina son yin aiki tare da shugaba Ouattara don zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashenmu biyu da kuma hada hannu wajen karfafa hadin kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














