A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Donald Trump murnar lashe zaben shugaban Amurka, yana mai fatan kasashen biyu za su lalubo hanya mai nagarta, ta yin tafiya tare a sabon zamani da ake ciki, ta yadda za su ci gajiyar hakan, da ma sauran sassan duniya baki daya.
Shugaba Xi ya ce tarihi ya nuna yadda Sin da Amurka suka ci gajiya daga hadin gwiwar su, da yadda suka yi hasara sakamakon fito na fito, don haka alaka madaidaiciya kuma mai dorewa tsakanin sassan biyu, na da fa’idar gaske ga cimma moriyar sassan biyu, da ma burikan daukacin al’ummun duniya.
- Xi Ya Bukaci Hubei Da Ya Rubuta Nasa Babi A Aikin Zamanantar Da Kasa
- Babban Yayan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo Ya Rasu
Kaza lika, shugaban na Sin ya bayyana fatan ganin kasashen biyu sun martaba ka’idojin girmama juna, da zaman lafiya, da hadin gwiwar cimma moriya tare, da karfafa shawarwari da tattaunawa, da shawo kan banbance banbancen su, da fadada cin gajiyar juna.
A dai yau din, shi ma mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya mika sakon taya murna ga J.D. Vance, bisa nasarar da ya yi ta zama sabon mataimakin shugaban kasar Amurka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)