Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Mahamat Idris Deby Itno, murnar lashe zaben shugaban kasar jamhuriyar Chadi.
Xi Jinping ya ce a shekarun baya-bayan nan, dangantakar Sin da Chadi ta ci gaba da habaka, kana aminci a tsakaninsu ya kara zurfi, kuma hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban na ta samun ci gaba, baya ga kara hadin kai da suke yi kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa.
Ya ce yana daukar batun raya dangantakar Sin da Chadi da muhimmanci, kuma a shirye yake ya hada hannu da shugaba Mahamat Deby, wajen karfafa goyon bayan juna da inganta hadin gwiwar abota a tsakaninsu, ta yadda al’ummominsu za su kara cin gajiyarsa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp