Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a ci gaba da kokarin inganta fannin aikin gona mai sigar musamman ta kasar Sin, a wani muhimmin taron ayyukan raya yankunan karkara, wanda aka gudanar daga ranar Jumma’a zuwa Asabar a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.Â
Kasar Sin, mai yawan jama’a biliyan 1.4, wato kusan kashi 1 bisa 5 na al’ummar duniya, tana da kashi 9 cikin 100 na filayen noma a duniya. Mafi yawan abincin da ake samarwa daga gonakin kasar Sin ne.
Bisa la’akari da karancin albarkatun da kasar ke da shi da kokarin kasar na samun kyakkyawar alaka tsakanin ‘yan Adam da muhalli, ya sa shugaba Xi ya bukaci daukar hanyar da ta dace da yanayin da kasar ke ciki, maimakon kwaikwayon kwarewa kai tsaye daga sauran kasashen dake da karfi a fannin aikin gona.
Taron na shekara-shekara wanda Xi ya jagoranta, ya samu halartar wakilan zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS. A yayin taron na yini biyu, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin samun isasshen abinci, da samar da isassun kayayyakin amfanin gona a kasuwa, yana mai jaddada kiran farfado da yankunan karkara, wajen kara habaka kasuwanni da ci gaban kauyuka.
Xi ya bayyana cewa, kiyaye samun isasshen abinci, da tabbatar da samar da muhimman kayayyakin amfanin gona cikin aminci, su ne muhimman al’amurra na farko wajen karfafa fannin aikin gona na kasar Sin. Shugaba Xi, ya kuma bukaci da a sake yin wani sabon zagaye na inganta noman hatsi tare da daukar matakai masu tsauri.
A yayin taron, Xi ya yi kira da a inganta filayen noma na asali na kasar zuwa filayen gonaki masu inganci akai-akai. Alkaluma na hukuma sun nuna cewa, nan da karshen shekarar 2022, filayen noman kasar masu inganci, za su kai kimanin kadada miliyan 66.67 (Ibrahim)