Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azamar cimma sabbin nasarori, wadanda za su zamo abun tunawa a tarihi cikin tsawon lokaci, kana a cika burikan al’umma, yayin da ake kokarin gina kasar gurguzu ta zamani a dukkanin fannoni.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar, ya yi wannan tsokaci ne a yau Litinin, a babban dakin taruwar jama’a dake nan birnin Beijing, yayin taron cikar tsohon shugaban majalisar wakilan jama’ar kasar Sin marigayi Qiao Shi shekaru 100 da haihuwa. (Saminu Alhassan)