Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen kaiwa ga sabon matakin ci gaba mai tsari, a yankin biranen Beijing da Tianjin da Hebei, kana a mayar da yankin misali na cimma nasarar zamanantarwa irin ta kasar Sin.
Shugaba Xi, ya yi wannan kira ne yayin da yake rangadi a lardin Hebei, inda kuma ya jagoranci zaman tattauna dabarun bunkasa ci gaba mai tsari a yankin na Beijing da Tianjin da Hebei.
Yayin taron, Xi ya yi kira ga lardin Hebei, da ya mayar da hankali ga muhimmin aikin sa na samar da ci gaba mai inganci, da samar da sabon salon ci gaba, ta yadda hakan zai ingiza kasancewar lardin babbar cibiyar raya tattalin arziki mai managartaccen yanayi.
Kaza lika, shugaba Xi ya ce tun bayan babban taron wakilan JKS na 19 da ya gudana a shekarar 2017, an cimma managarcin ci gaba, a fannin samar da ci gaba mai tsari a yankin Beijing da Tianjin da Hebei, musamman ma a sabon yankin Xiongan.
Daga nan sai ya bayyana cewa, kwamitin kolin JKS, ya taka muhimmiyar rawa wajen raya matakan ci gaba daga dukkanin fannoni, wanda hakan ya biya bukatun ci gaba mai inganci na kasar Sin a sabon zamani, kuma wadannan dabaru sun zamo muhimmin tafarki, na ingiza zamanantar da kasar Sin. (Saminu Alhassan)