Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a zage damtse wajen tabbatar da an kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yayin da ake fuskantar kalubalen ambaliyar ruwa, da sauran bala’u masu nasaba da hakan a wasu sassan kasar Sin.
Xi, ya gabatar da muhimmin umarnin ne dangane da ayyukan da ake gudanarwa na dakile tasirin ambaliyar ruwa, da samar da agaji ga wuraren da ibtila’in ya aukawa.
Shugaban na Sin ya ce, ya zama wajibi a gudanar da dukkanin ayyukan da suka kamata, don bincike da ceton rayukan jama’a da suka bace, ko suka makale a wuraren da ambaliya ta auku, kana a gaggauta mayar da wadanda ka iya fadawa yanayin ambaliyar ruwa zuwa wurare masu tsaro domin takaita asarar rayuka.
Rahotanni daga hukumar shawo kan ambaliyar ruwa ta birnin Beijing na cewa, mutane 30 sun rasa rayukansu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya sauka a daren jiya Litinin. Hukumar ta ce, cikin adadin, mutune 28 sun rasu ne a gundumar Miyun, da mutum biyu a gundumar Yanqing, wuraren dake arewacin birnin masu makwaftaka da tsaunkuna.
Tuni aka sauyawa jimillar mutane 80,332 matsugunai, bayan da ma’aunin yawan ruwan da ke sauka ya kai milimita 543.4 a gundumar Miyun inda ruwan saman ya fi tsananta. An ce, mamakon ruwan saman ya lalata sassan hanyoyi 31, tare da katse lantarki a wasu kauyuka 136. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp