Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci lardin Zhejiang dake gabashin kasar da ya yi kokarin rubuta sabon babi na ciyar da zamanantarwar kasar Sin gaba.
Xi, ya yi wannan kira ne a ziyarar da ya kai Zhejiang daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Satumba.
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Tattauna Dauwamammen Ci Gaban Aikin Sufuri
- Kasar Sin Ta Aike Da Kayayyakin Agajin Gaggawa Zuwa Kasar Libya Da Ambaliyar Ruwa Ta Afkawa
Xi ya bukaci lardin da ya maida hankali kan gina wani yanki da zai zama abin nuni na samun wadata tare da mayar da kansa wani muhimmin misali da ke nuna karfin tsarin gurguzu mai dauke da halayen kasar Sin a sabon zamani.
A yayin ziyarar tasa, Xi ya ziyarci biranen da suka hada da Jinhua da Shaoxing, inda ya duba wurare da suka hada da karkara, da kasuwar cinikayya, da dakin baje koli, da wurin shakatawa na al’adu.
Yayin da yake kan hanyarsa ta komawa birnin Beijing, Xi ya kuma ziyarci birnin Zaozhuang da ke lardin Shandong na gabashin kasar Sin. (Yahaya)